Fatawoyin Rahma - Tare Da Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo
2.96K subscribers
19 photos
24 videos
1 file
1.03K links
Amsa Fatawoyin Da Suka Shafi Addini Da Rayuwa Wanda Al-Duktuur Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo Yake Amsawa a Kowane Mako
Download Telegram
November 11, 2021
*Fatawoyin Rahma*

Lahadi 24/3/1443 = 31/10/2021

Tare da *Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo*

1. Ya hallata mai ɗaura bene a sama ya ƙara faɗin bene a sama domin samun yalwatacen ɗaki?

2. Menene matsayin bada 'mutuätu ɗalaƙ' (kyautar lallashi) ga matar da aka sake ta!

3. Mace da take da janaba sai jinin al’ada ya zo mata, za ta yi wankan janaba kafin ta gama al’adarta?

4. Hukuncin Mutumin da yake Limanci, ya ke karanta Alƙur'ani izu 20 ko wacce Rana a biya shi - zai kuma samu lada?

5. Hukuncin saukar Al-ƙur'ani ga mutum in ya mutu!

6. Mai ciwon ulcer da ya bige mutum ya mutu bisa kuskure ya ya zai yi?

7. Mata za su iya yiwa Mamaci Sallah kafin a fito da shi? Kuma za su iya bin jam’in Sallar Jana’iza da maza za su yi?

8. Ana rubutawa Mutum ladan kyakyawar niyya abin da Mutum bai samu damar aikatawa ba? Hakanan anan rubutawa Mutum zunubin abinda ya yi niyyar yi amma bai samu damar aikatawa ba?

9. Hukuncin wanda zai ba da kuɗi domin samun haƙƙin sa a gwamnatance!

10. Ma'aikacin Bankin Musulunci da ake buƙatar ya cika kuɗi in yayi kuskure a kirgen kuɗi zai iya amfani da kuɗi in kirgen da aka samu kuɗi da ya haura za su yi amfani da shi?

11. Wanda ya fara kasuwanci da Rîbà yaya zai tuba?

12. Mutumin da ya ba da bashi zai nemi ƙari?
Sannan wanda aka ba shi bashi zai iya bada ƙari da raɗin kansa?

13. Ya Halatta Mutum yayi yarjejeniya da Matarsa akan zata ɗauke masa bukatanta na yau da gobe domin ya bar ta ta yi aiki?

Domin Downloading Danna Link Dake Kasa 👇

https://darulfikr.com/s/127623


Vedion Shirin Fatawoyin Rahma Lahadi 👇

https://youtu.be/_VrxDVgn8j0

Domin Shafin Fatawoyin Rahma Na Facebook 👇

www.facebook.com/fatawoyinrahama

Ga mai son aikawa da tambaya sai ya rubuta ta saƙon kar ta kwana (text) ko saƙon WhatsApp ta 07036041455 ko ta email ta fatawoyinrahma@yahoo.com

Darulfikr taku ce domin yada Sunnah.
11/11/2021
November 11, 2021
*Fatawoyin Rahma*

Asabar 1/4/1443 = 6/11/2021

Shimfiɗa -Kiyaye Furuci ( Furuci da Baki Ko da Hoto)

Tare da *Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo *

Tambayoyi da Amsoshin da ke ciki:

1. Wanda ya ke magana lokacin Kiran Sallah ba zai iya furta Kalmar Shahada lokacin mutuwarsa?

2. In mutun yana Sallah ana sanya zunubansa akan kansa da kafaɗunsa in ya yi Sujjada da Ruku'o sai laifukansa su rinƙa kakkaɓewa?

3. Ya hallata Liman yayi kuskure da gangan domin koyarwa?

4. Hukuncin sauraron waƙa tare da yin Zikiri a lokaci guda

5. Hukuncin hadisin Mace da Mahaifinta ba yi da lafiya amma ba ta je duba shi ba saboda Mijinta ba ya nan. Bayan ya rasu, sai aka yafe masa saboda biyayyarta ga Mijinta!

6. Mace mai takaba za ta iya fita domin ta'aziyya a wani gari ko unguwa?

7. Ya inganta duk tafiyar da Mace za ta yi daga ɗakinta zuwa Kitchin za a rubuta mata ladan Umra!

8. Miji yana da haƙƙin yayiwa Matar sa Allah ya isa in ta kwana da yunwa alhali akwai abincin dafawa!

9. Akwai hâdisin da yake nuna Annabi yana taimakawa Iyalansa aikin gida!

10. Shin adadin Annabawa da Manzanni

11. Ya inganta lokacin da Annabi Sulaiman ya rasu Gara ce ta nunawa Aljanu ya rasu?

12. Abinda ya ke haifar da cuttutukan zuciya da abinda zai magance su!

Domin Downloading Danna Link Dake Kasa 👇

https://darulfikr.com/s/127624


Vedion Shirin Fatawoyin Rahma Asabar 👇

https://youtu.be/WMfXHmd2pYE

Domin Shafin Fatawoyin Rahma Na Facebook 👇

www.facebook.com/fatawoyinrahama

Ga mai son aikawa da tambaya sai ya rubuta ta saƙon kar ta kwana (text) ko saƙon WhatsApp ta 07036041455 ko ta email ta fatawoyinrahma@yahoo.com

Darulfikr taku ce domin yada Sunnah.
11/11/2021
November 11, 2021
*Fatawoyin Rahma *

Lahadi 2/4/1443 = 7/11/2021

Tare da Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo

Tambayoyi da Amsoshin da ke ciki:

1. Saya ko sayar da gwal ga wanda bai san farashin sa ba.

2. Ya hallata Sojoji masu yaƙi da 'yan ta'adda su ɗebe kayan ganimar 'yan ta'adda da suke yaƙar su?

3. Ya hallata Jami'an an 'Yansanda (stop and search) su karɓi kyauta daga masu safara kaya ba tare da sun san abin da suke ɗauke da shi cikin motar su?

4. Mutum zai iya sadaƙatul Jariya ga Iyayensa da suke da rai?

5. Ya hallata ' Yan uwa da za su gaji 'yar uwarsu su haɗu su yi sadaƙa da abin da ta bari domin ladan yaje mata?

6. Wanda ya rabu da uwarsa ba da daɗi ba, zai iya yin wani aikin da zai cece shi a wajen Allah?

7. Makomar wanda ya rasu a wajen dambe!

8. Ya hallata Miji ya ƙara Aure ba tare da sanin Uwargida ba!

9. Nafilfili da Annabi ﷺ ba ya bari koda a halin tafiya!

10. Mamu za su bayyana Kabbara in Liman ya yi Kabbara?

11. Mutum zai iya sanya hannunsa su wuce gwuiwar sa domin bayansa ya miƙe daidai a Ruku'u?

12. Sallama Uku ya tabbata a Sunna?

13. Dole Mutun sai ya je Sallah a Massalacin da yake da tazara da in da yake?

14. Ya inganta Sallar Juma'a da aka yi da rawani tafi wanda aka yi ba rawani da daraja 70?

15. Lokacin fitar Sallar Îshâ!

16. Mamü zai yi Sujjadar Rafkanwa idan ya yi Sujjada kafin Liman, da kuskure?

17. Ya hallata mai Sallah da zanin da ke da najasa ta yafuto wani zani mai tsafta sannan ta ci gaba da sallarta ko da ta karkace wa alƙibla?

18. Hukuncin Masu sana'ar goge takalma yayin huɗubar Jumu'a!

19. Matsayin Mamun da yaro ya hau kan shi bai iya bin Liman ba. Abin da ya tsere masa zai ciko?

20. Gaskiya ne Magidancin da yayi Zina ya zama Mushe? Allah ba zai karɓi duk wani aiki ko tubansa ba?

21. Wanda ya yi Zina an cire masa rigar Imani?

22. Mahaifiyar da take ƙyamar ‘yar ta ta sa Niƙabi!

23. Wanda ya sayar da fili zai ba da Zakka ko sai kuɗin ya shekara?

24. Hukuncin kyautar da za a bawa mai aski ko man fetur bayan mutum ya biya Kamfani?

25. Alƙalai masu ɗaukar wani kaso na dukiyar marayu in sun raba, suna da wata hujja ce?

26. Ɗalibi zai iya rage shekaru domin ya samu damar zuwa Hidimar ƙasa (NYSC)

Domin Downloading Danna Link Dake Kasa 👇

https://darulfikr.com/s/127626

Vedion Shirin Fatawoyin Rahma Lahadi 👇

https://youtu.be/5SGmW_CjICM

Domin Shafin Fatawoyin Rahma Na Facebook 👇

www.facebook.com/fatawoyinrahama

Ga mai son aikawa da tambaya sai ya rubuta ta saƙon kar ta kwana (text) ko saƙon WhatsApp ta 07036041455 ko ta email ta fatawoyinrahma@yahoo.com

Darulfikr taku ce domin yada Sunnah.
11/11/2021
November 11, 2021
KYAUTATA MU'AMALA CIKIN DUKKANIN AYYUKA

KHUDBAR SALLAR JUMU'A

Tare da
Dr. Abubakar Mohammad Sani Birnin-Kudu (Hafizahullah)
@
Dutse Central Mosque,
Jihar Jigawa Nigeria.

Jumu'a :

👇👇👇

https://darulfikr.com/s/127714


Ayi sauraro lafiya

Darulfikr taku ce domin yada Sunnah.
13/11/2021
November 13, 2021
(Hukuncin Kallon Fina-Finan Dake Nuna Tarihin Annabawa)

Daga Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Shirin da yake amsa tambayoyin da kuka aiko zuwa cikin shirin Fatawoyin Rahma Daga Gidan Radio Na Rahma Radio Kano 👇

https://youtu.be/c4E4wA6t0FM

Ayi sauraro lafiya
November 16, 2021
Amsoshin tambayoyin da kuka aiko mana

Tare Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Shirin da yake amsa tambayoyin da kuka aiko zuwa cikin shirin Fatawoyin Rahma Daga Gidan Radio Na Rahma Radio Kano 👇

https://youtu.be/e9JhC6ALt5o

Ayi sauraro lafiya
November 17, 2021
Hukuncin Karanta Suratul Kahfi Duk Ranar Juma'a


Tare Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Shirin da yake amsa tambayoyin da kuka aiko zuwa cikin shirin Fatawoyin Rahma Daga Gidan Radio Na Rahma Radio Kano 👇

https://youtu.be/yzSVZC21xi4

Ayi sauraro lafiya
November 19, 2021
November 20, 2021
Fatawoyin Rahma Lahadi 21-11-2021

Tare da Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Amsoshin tambayoyin ku da kuka aiko zuwa cikin shirin Fatawoyin Rahma Daga Gidan Radio Na Rahma Radio Kano 97.3 FM wanda Anas Idris Hassan Yake karanta tambayoyin

Domin Sauraro Danna Link 👇

https://youtu.be/WT73SBB86C4

Ayi sauraro lafiya
November 21, 2021
*Fatawoyin Rahma Asabar* 16/4/1441 = 20/11/2021

Tare da *Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo *

Shimfiɗa - Faɗin Allah:

فَهَلْ عَسَيْتُمْ إِن تَوَلَّيْتُمْ أَن تُفْسِدُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ وَتُقَطِّعُوٓا۟ أَرْحَامَكُمْ

Tambayoyi da Amsoshin da ke ciki -

1. Ya hallata Mutum ya bada takardar aiki da ya samu ga wani?

2. Wanda aka yi masa kyauta da kuɗin marayu alhali bai sani ba sai bayan da yayi amfani da kuɗin, yana da laifi?

3. Wanda ya ke saɓawa mahaifiyar sa zai iya shiga cikin kuncin rayuwa a duniya?

4. Hukuncin yiwa Shugaba mummunar addu'a.

5. Hukuncin cin dabbar da mota ta kaɗe aka yanka ta kafin ta mutu?

6. Hukuncin wanda ya karɓi taimakon Gina Makaranta daga wanda yake caca.

Domin Downloading Danna Link Dake Kasa 👇

https://darulfikr.com/s/128095


Vedion Shirin Fatawoyin Rahma Asabar 👇

https://youtu.be/cwLZgy5cB2c

Domin Shafin Fatawoyin Rahma Na Facebook 👇

www.facebook.com/fatawoyinrahama

Ga mai son aikawa da tambaya sai ya rubuta ta saƙon kar ta kwana (text) ko saƙon WhatsApp ta 07036041455 ko ta email ta fatawoyinrahma@yahoo.com

Darulfikr taku ce domin yada Sunnah.

21/11/2021
November 21, 2021
( Dalilin Lalacewar Zamantakewa A Bayan Ƙasa)

Tare Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Shirin da yake amsa tambayoyin da kuka aiko zuwa cikin shirin Fatawoyin Rahma Daga Gidan Radio Na Rahma Radio Kano 👇

https://youtu.be/sJVRcZmnCeM

Ayi sauraro lafiya
November 22, 2021
*Fatawoyin Rahma *

Lahadi. 16/4/1441 = 21/11/2021

Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo

Shimfiɗa : _Kyautata ma Al'uma Lokacin Tsanani da Kuncin Rayuwa_

Tambayoyi da Amsoshin da ke ciki -

1. Ya hallata Mutum ya yi ' Transfer' na kuɗi da ƙari ga wanda ya zo neman kuɗi a hannunsa?

2. 'Ya za ta iya kai Mahaifiyar su Kotu in ba ta son a raba musu gadon gidan su?

3. Hukuncin yaji ƙin cin abinci!

4. Hukuncin wanda yayi alwala sannan ya taka najasa!

5. Hukuncin wanda yayi Sallah ba tare da Shafan Kai ko Kunne!

6. Mutumin da yake Sallah yake karanta Fatiha zai iya adduar buƙata yayin da ya zo gaɓan 'Iýýaka Na'abudu Wa Iýýaka Nasta'in'?

7. Hukuncin siyan kayan abinci da sauƙi domin a ɓoye sai ya yi tsada.

8. Ya tabbata ƙananan yara da suka rasu suna ƙarƙashin kulawar Annabi Ibrahim a Barzahu?

9. Mutum zai iya fitar da Zakka ya bawa yarsa wata -wata?

10. Kirista zai iya zama wakilin Musulmi ya karɓa masa Aure?

11. Akwai banbanci cewa ' Miji yafi girman haƙƙi akan Iyaye da cewa Miji yafi daraja akan Iyaye'?

12. In Mace taga mutumin kirki za ta iya roƙon Allah ya sa ya aureta?

13. Ya hallata mai kiwon Kaji ya siyarwa mai yin Kirsimeti?

14. Ya hallata cin naman Kada?

15. Ana yin Shafa'i da Witr bayan ƙetowar Alfijir?

16. Matsayin Sallar wanda yayi Sahu da wanda ya sha giya yayi manƙas!

17. Hukuncin faɗin Àmeen (a Sallah ko wajen Sallah) a ayoyin ƙarshe na Baƙara.

18. Wanda ya yi alwala ya ci abu ba tare da ya kurkure bakinsa ba, ya na da alwala?

19. Matsayin zuwa Sallah a guje

20. Hukuncin makara zuwa Sallar Asuba a Jam'i

21. Zikirin da ake yi 33 bayan Sallar Farilla ya inganta ana yin ƙasa da haka?

22. Adduar ziyarar maƙabarta

23. Hukuncin tashi tsaye domin zuwan wani ko girmama wani!

Domin Sauraro Danna Link Dake Kasa 👇

https://darulfikr.com/s/128129


Vedion Shirin Fatawoyin Rahma Lahadi 👇

https://youtu.be/WT73SBB86C4

Domin Shafin Fatawoyin Rahma Na Facebook 👇

www.facebook.com/fatawoyinrahama

Ga mai son aikawa da tambaya sai ya rubuta ta saƙon kar ta kwana (text) ko saƙon WhatsApp ta 07036041455 ko ta email ta fatawoyinrahma@yahoo.com

Darulfikr taku ce domin yada Sunnah.
23/11/2021
November 23, 2021
( Kyautatawa Lokacin Tsanani Da Ƙuncin Rayuwa )

Tare Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Shirin da yake amsa tambayoyin da kuka aiko zuwa cikin shirin Fatawoyin Rahma Daga Gidan Radio Na Rahma Radio Kano 👇

https://youtu.be/ezvPSVHHpsU

Ayi sauraro lafiya
November 23, 2021